Isa ga babban shafi
Coronavirus

Yawan rayukan da coronavirus ke halakawa a duniya ya doshi dubu 290

Alkalumman hukumomin lafiya a yau Litinin sun nuna cewa, yawan mutanen da annobar COVID-19 ta halaka a fadin duniya ya haura dubu 283, yayinda wasu sama da miliyan 4 suka kamu da cutar.

Likitoci tare da wani da ya kamu da cutar coronavirus a asibitin Jami'ar Strasbourg a Faransa.
Likitoci tare da wani da ya kamu da cutar coronavirus a asibitin Jami'ar Strasbourg a Faransa. AFP
Talla

A halin yanzu annobar ta coronavirus ta lakume rayuka dubu 283 da 978, daga cikin akalla mutane miliyan 4 da dubu 148 da 350 da suka kamu da cutar, a jumillar kasashe da manyan yankunan duniya 195.

Daga cikin adadin wadanda suka kamun kuma, akalla miliyan 1 da dubu 396 da 200 sun warke.

Annobar tafi barna a Amurka fiye da kowace kasa a duniya inda ta kashe mutane dubu 79 da 894, sai Birtaniya da ta rasa mutane dubu 32 da 065, biye kuma Italiya ce, inda annobar at COVID-19 ta kashe mutane dubu 30 da 739.

A Spain mutane dubu 26 da 744 suka mutu, a Faransa kuma dubu 26 da 643 suka mutu a dalilin cutar, sai nahiyar Afrika inda annobar ta halaka mutane dubu 2 da 318.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.