COVID-19 ta lakume sama da rayuka dubu 280 a sassan duniya
Adadin mutanen da annobar coronavirus ko COVID-19 ta kama a duniya ya zarce miliyan 4, yayin da sama da 280,000 suka sheka lahira, kana sama da miliyan guda suka warke.
Wallafawa ranar:
Alkaluman da hukumar lafiya ta duniya ta gabatar a daren alhamis din nan sun nuna cewar mutane miliyan 4 da dubu 70, 660 suka kamu da cutar a fadin duniya, yayin da 280,693 suka mutu, kana miliyan guda da dubu 354,100 suka warke gaba daya.
Har yanzu kasar Amurka ke gaba wajen yawan mutanen da suka mutu, inda take da 79,058, daga cikin miliyan guda da 321,223 da suka kamu, yayin da 212,534 suka warke.
Birtaniya ke matsayi na biyu da mutane 31,855 da suka mutu daga cikin 219,183 da suka harbu da cutar, sai Italia da tayi asarar mutane 30,560, yayin da Spain tayi asarar mutane 26,621, sai kuma Faransa mai mutane 26,380.
A nahiyar Turai kawai, mutane 156,111 suka mutu, sai Amurka da Canada mai mutane 83,868 sannan Afirka mai mutane 2,261.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu