Annobar corona ta lakume sama da rayuka dubu 271 a duniya
Sabbin alkalumman da hukumomin lafiyar kasa da kasa suka fitar a baya bayan nan, sun nuna cewa adadin mutanen da annobar coronavirus ko COVID-19 ta halaka a fadin duniya ya kai dubu 271, da 780, daga cikin jumillar mutane miliyan 3 da dubu 896 da 790 da suka kamu da cutar.
Wallafawa ranar:
Sabon rahoton yace sama da kashi 85 cikin 100 na mutanen da suka mutu, daga nahiyar Turai da Amurka suke.
A jumlace annobar coronavirus ta halaka mutane sama da dubu 153 a Turai, daga cikin akalla miliyan 1 da dubu 678 da suka kamu.
Amurka ce kuma kasar ta annobar ta fi yiwa barna a dunya, bayan kashe mata mutane dubu 76 da 101, sai Birtaniya mai mutane dubu 31 da 241, Italiya ta rasa mutane dubu 30 da 201, Spain mutane dubu 26 da 299 sai kuma Faransa da cutar ta halakawa mutane dubu 26 da 230.
A nahiyar Afrika jumillar mutane dubu 2 da 105 annobar coronavirus ta kashe, daga cikin mutane dubu 54 da 944 da suka kamu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu