Adadin mutanen da COVID-19 ta halaka a duniya ya zarta dubu 260
Hukumomin lafiya na kasashen duniya sun ce sabbin alkalumman da suka tattara ya nuna cewa Annobar COVID-19 ta kashe mutane dubu 260 da 546.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sama da mutane milyan 3 da dubu 710 da wasu mutanen 240 ne wannan cutar ta kama a kasashe 195, duk da cewa milyan 1 da dubu 153 har ma da wasu mutane 300 daga cikinsu, sun warke daga cutar.
Kafin tsakiyar daren laraba, coranvirus ta kashe kusan mutane dubu 72 a Amurka, sannan sama da dubu 189 suka warke, yayin da annobar ta kasance ajalin mutane sama da dubu 32 a kasar Birtaniya.
A Italiya, kasa ta 3 da cutar ta fi yi wa ta'adi, an samu asarar rayukan mutane dubu 29 da 684, sai kuma Spain an samu mamata dubu 25 da 857, sannan a Faransa inda Covid-19 ta dauke rayukan mutane dubu 25 da 809.
Kafin tsakiyar daren na ranar, alkalumma sun nuna cewa daga cikin mutane dubu 50 da 413 da ta kama a Afrika, annobar ta kashe dubu 1 da 996 a nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu