Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta kashe mutane kusan dubu 255 a sassan duniya

Daga bullarta a watan disambar da ya gabata na 2019 zuwa tsakiyar daren jiya, annobar Coronavirus ta halaka mutane kusan dubu 255 a sassan duniya.

Jami'an lafiya a asibitin garin Magdebourg, yayin kokarin ceto ran wani mai dauke da cutar coronavirus.
Jami'an lafiya a asibitin garin Magdebourg, yayin kokarin ceto ran wani mai dauke da cutar coronavirus. AFP/Ronny Hartmann
Talla

Mutnane milyan 3 da dubu 629 da 160 ne aka tabbatar da cewa cutar ta kama a kasashe 195, duk da cewa akwai wasu dimbin mutanen da ba a kai ga yi wa gwajin cutar ba a sassan duniya.

Sai dai kamar yadda alkalumman hukumar lafiya ta duniya suka nuna, sama da mutane milyan 1 da dubu 124 da 600 sun warke daga cutar.

Amurka, kasar da ta samu mutum na farko da ya kamu da COVID-19 a farkon watan fabarairu, ta yi rasa mutane dubu 70 da 115 da annobar ta kashe, wasu sama da dubu 187 suka warke a kasar.

Birtaniya ce kasa ta biyu da annobar ta fi halakawa jama’a inda sama da mutane dubu 32 suka mutu, sai Italiya mai mutane dubu 29 da 315, yayin da Spain ta rasa mutane dubu 25 da 613, sai kuma Faransa inda aka samun asarar rayuka dubu 25 da 531.

A nahiyar Afrika, zuwa tsakiyar daren jiya, coronavirus ta kashe mutane dubu 1 da 894.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.