Isa ga babban shafi
Duniya

COVID-19 ta lakume sama da rayuka dubu 250 a duniya

Alkalumman hukumar Lafiya ta Duniya sun nuna cewar mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da annobar coronavirus a duniya sun zarce dubu 250 yayinda mutane sama da miliyan guda suka warke.

Wasu jami'an lafiya dauke da gawar wani da annobar coronavirus ta kashe a birnin Birmingham dake Birtaniya. 21/4/2020.
Wasu jami'an lafiya dauke da gawar wani da annobar coronavirus ta kashe a birnin Birmingham dake Birtaniya. 21/4/2020. REUTERS/Carl Recine
Talla

Alkalumman na nuna cewa sama da mutane milyan 3 da dubu 555 sun kamu da cutar a sassan duniya, amma akwai wasu mutanen miliyan daya da dubu 88 da 900 da suka warke har ma suka koma a cikin iyalansu.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, coronavirus ta sake kama mutane dubu 73 da 568 tare da kashe dubu 3 da 511 a duniya.

A cikin wadannan sa'o'i 24 na baya bayan nan, annobar ta fi yin kisa ne a kasashe 3, domin kuwa ta dauke rayuka sama da dubu daya da 130 a Amurka, a Birtaniya mutane 306 yayin da a Faransa ta kashe 288.

Daga cikin mutane dubu 250 da suka mutu a sassan duniya, sama da dubu 145 a nahiyar Turai ne, dubu 72 a kasar Amurka da Canada, dubu 7 da 100 a Yankin Gabas ta Tsakiya, yayinda nahiyar Afrika ta yi asarar mutane dubu 1 da 835 daga farkon annobar zuwa yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.