Maganin Remdesivir na iya kawo karshen coronavirus - Amurka
Mai yiwuwa hukumomin Amurka su bada umurnin amfani da maganin Remdesivir domin amfani da shi wajen kawo karshen cutar coronavirus, wadda ta halaka mutane sama da dubu 60,000 a fadin kasar.
Wallafawa ranar:
Yayin sanar da shirin, shugaban hukumar yaki da cututtuka ta Amurka Anthony Fauci, ce binciken da kwararru suka gudanar kan maganin na Remsesivir, ya nuna cewar, marasa lafiya ko masu dauke da cutar coronavirus da suka sha maganin, sun fi saurin samun waraka, sama da marasa lafiya da basu sha maganin ba.
Shugaban hukumar yaki da yaduwar cutukan ta Amurkan yace kimanin marasa lafiya dubu 1 da 90 ne suka bada damar yin gwajin sabon maganin akansu.
Sai dai hukumar lafiya ta duniya WHO, tace yayi wuri a cimma matsaya ga gwajin sabon maganin na Remdesivir da Amurka ta yi.
Remdesivir na cikin jerin magungunan da a yanzu kwararru a sassan duniya suka dukufa wajen bincike akansu, domin samar da maganin cutar murar coronavirus, da kawo yanzu ta halaka sama da mutane dubu 227 tare da kama wasu sama da miliyan 3, bayan ratsa kasashe 193.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu