Isa ga babban shafi

Coronavirus ta halaka Amurkawa kusan dubu 2 a kwana 1

Sabuwar kididdigar da hukumomin lafiya suka fitar ta ce yawan mutanen da annobar coronavirus ta halaka a duniya ya karu zuwa sama da dubu 214, yayinda sama da mutane miliyan 3 suka kamu da cutar.

Wasu jami'an kiwon lafiya a Amurka yayin daukar wani da ya kamu da cutar COVID-19 a Boston dake Massachusetts. 3/4/2020.
Wasu jami'an kiwon lafiya a Amurka yayin daukar wani da ya kamu da cutar COVID-19 a Boston dake Massachusetts. 3/4/2020. REUTERS/Brian Snyder
Talla

Sai dai kawo yanzu sama da mutane dubu 840 sun warke daga cutar.

Zuwa wayewar garin yau laraba hukumomin lafiya sun tabbatar da cewar annobar coronavirus ta lakume rayuka dubu 214 da 451, bayan kama sama da mutane miliyan 3 da dubu 68 da 330, daga cikinsu kuma mutane dubu 840 da 300 sun katarin warkewa.

Cikin sa’o’i 24 da suka gabata mutane dubu 1 da 970 annobar ta halaka a Amurka kadai, sai kuma 586 a Birtaniya, yayinda Italiya ta rasa mutane 382.

Har yanzu Amurka ke kan gaba tsakanin kasashen da annobar tafi yiwa barna, bayan halaka mata mutane dubu 57 da 533 a jimlace, sai Italiya da cutar ta kashewa mutane dubu 27 da 359, Spain ke biye bayan rasa mutane dubu 23 da 822, biye da ita kuma Faransa ce da ta rasa mutane dubu 23 da 660, sai kuma Birtaniya inda cutar ta lakume rayuka dubu 21 da 678.

A karshe nahiyar Afrika ta rasa jimillar mutane dubu 1, da 502, daga cikin dubu 34 da 155 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.