Isa ga babban shafi

Shugaban club din Olympiacos ya kamu da coronavirus

Mamallakin kwangiyoyin kwallon kafar guda biyu, Nottingham Forest da Olympiakos, Evangelos Marinakis ya kamu da cutar coronavirus.

Mamallakin club din Olympiacos Evangelos Marinaki
Mamallakin club din Olympiacos Evangelos Marinaki Reuters
Talla

Marinakis, mai shekaru 52, ya halarci wasan da kungiyar sa Forest ta fafata a filin City Ground dake Ingila da Milwall ranar Jumma’a a Gasar League.

Bayan komawar sa Girka daga Ingila ne aka gano ya kamu da cutar, duk da cewa lokacin da yake can Nottingham alamun cutar basu bayyana ba a tare da shi.

Marinakis da kansa ya bayyana kamawu da cutar ta shafin sa na Istagaram bayan gwajin da akayi masa. Yana mai cewa "cutar zamani ta kamani, kuma ya zama wajibi na sanar da al’umma halin da nake ciki,amma yanzu haka ina samun sauki, sakamakon shawarwarin likita na da nake amfani da shi".

Yanzu haka mamyan jami’an da suka wakilci club din Millwall, da ya lallasa Nottingham da ci 3 da 0 a wasan na ranar Juma'a a, sun killace kansu sakamakon mu’amala da suka yi da Marinakis lokacin wasan.

Wasa tsakanin Manchester City da Arsenal a wasaninin Firimiya da ya kamata a kara a daren Laraban nan ma an dage, bayan sanarwar cewa Evangelos Marinakis ya kamu da cutar coronavirus.

Club din Olympiakos na kasar Girka, ya kara da Arsenal kwanaki 16 da suka gabata lokacin da  a filin wasan Emirate wato a wasan gasar Europa, Marinakis ya kasance filin wasan kuma ya gana da dama daga cikin shugabanni da ‘yan wasan Arsenal.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.