Harin Amurka a Afghanistan ya kashe ‘Yan IS da dama
Amurka ta yi amfani da bam dinta mafi girma wanda ba na nukiliya ba akan mayakan IS, a wani wuri da ke gabashin kasar Afghanistan, wani abu da ake kallo a matsayin daukar fansa dangane da kashe wani jami’in sojin kasar daya a karshen makon jiya.
Wallafawa ranar:
Wannan bam da aka bayyana cewa nauyinsa ya fi ton 10, Amurka ba ta taba yin amfani da shi a fagen yaki ba sai a wannan karo, inda ma’aikatar tsaron kasar ta ce ya hallaka ‘yan ta’addan IS 36.
Shugaba Donald Trump ya ce abubuwan da suka faru a cikin makwanni 8 sun sha bamban da wadanda suka faru a cikin shekaru 8 da suka gabata.
A cikin sanarwar da ta fitar, Ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce harin bai yi lahani ba ga fararen hula.
An jefa Bam din sanfurin GBU-43-B daga jirgin yakin Amurka akan IS a yankin Achin a daidai karfe bakwai da rabi na yamma agogon kasar Afghanistan a jiya Alhamis.
Bam din na da nauyin da ya kai kilogram dubu tara da dari takwas.
Janar John Nicholson kwamandan rundunar sojin Amurka a Afganistan ya ce mayakan kungiyar IS sun kara karfafa tsaronsu ta hanyar samun mafaka a mabuyar da ke karkashin kasa abin da ya sa jefa irin wannan kirar bam din ya zama dole don tarwatsasu a yakin da Rundunar sojin kasar ke yi na kawo karshen mayakan kungiyar da ayyukansu ya janyo asarar rayukan mutane da dama a Iraqi da Syria da kuma Afghanistan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu