Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kai harin kunar bakin wake a Kotun Kolin Afghanistan

Wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane 19 bayan ya tayar da bom a kotun Kolin Afghanistan da ke Kabul a yau Talata. Harin ya kuma raunana mutane 41.

Mutane kusan 20 suka mutu a harin kunar bakin wake da aka kai a kotun Koli a Kabul
Mutane kusan 20 suka mutu a harin kunar bakin wake da aka kai a kotun Koli a Kabul REUTERS
Talla

Cikin wadanda suka jikkata sun hada da mata da yara.

Ministan cikin gidan kasar ya ce, maharin ya tayar da bama-baman da ke jikinsa ne a harabar ajiye motoci, a dai dai lokacin da ma’aikata ke shiga mota bayan sun tashi daga aiki.

Ko a watan jiya, sai da kungiyar Taliban ta kai makamancin wannan harin a wani ofishin majaliasar wakilan kasar, inda ta kashe mutane 30 tare da jikkata 80.

Afghanistan dai na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro daga mayakan Taliban da al Qaeda da kuma IS bayan ficewar sojojin kungiyar tsaro ta NATO a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.