Isa ga babban shafi
Afghanistan

Dubban Sojojin bogi na karbar albashin Amurka a Afghanistan

Amurka ta ce akwai dubban sojojin boge da ke karbar albashin da ta ke biyan Jami’an tsaron Afganistan kuma suna sayarwa kungiyar Taliban da makaman da Amurka shigar a kasar.

Sojojin Afghanistan da ke fada da Taliban
Sojojin Afghanistan da ke fada da Taliban REUTERS/Stringer
Talla

Zancen sojojin bogi masu karbar albashi abu ne da aka dade ana danbarwa akai ganin kungiyar tsaro ta NATO da Amurka sun jima suna zargin rashawa a ma’aikatar tsaron kasar Afghanistan.

Janar John Sopko manzon Amurka na musamman kan sake gina Afghanistan ya zargi Kwamandojin kasar da soke kudaden Sojojin na Bogi da Amurka ke biya albashi wadanda ya ce sun zarce dubu 10.

Akwai kuma batun yadda mayakan Taliban ke sayen makamai da man fetur da kuma albarusai daga hannun dakarun Afghanistan.

Batun rashawa a tsakanin sojin Afghansitan al’amari ne da aka dade ana kokarin magancewa tun bayan da Amurka ta jagoranci mamayar kasar da niyar sake gina barnar da mayakan Taliban suka aikata.

A shekarar 2015 ne ‘yan sanda da dakarun sojin kasar ta Afghanistan suka karbi ikon tsaro daga hannun kungiyar tsaro ta NATO.

Rahoton binciken da Janar Sopko ya gabatar a Washington na zuwa ne kafin Donald Trump ya karbi ragamar shugabanci a Amurka, kuma Sopko ya ce yana da wahala sabon shugaban ya iya magance rikicin Afghanistan kamar yadda Obama ya yi iya na shi kokari a shekaru 8.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.