Isa ga babban shafi
Afghanistan

Wani jigo a kungiyar Taliban ya rasu

Wani harin sojin Amurka ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin manyan kwamandojin Taliban a kasar Afghanistan.Rundunar Sojin Amurka na taka rawa a yakin kasar Afghanistan.

Harin bam a Afghanistan
Harin bam a Afghanistan REUTERS/Mohammad Ismail TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar Mullah Abdul Salam Ahkund wanda ke kiran kansa gwamnan Lardin Kunduz bayan wani hari da ake jin cewa sojojin Amurka ne suka kai shi.

Amurka na daga cikin kasashen dake kokarin sake dawowa da zaman lafiya  a kasar ta Afghanistan ,kasar da aka share tsawon shekaru ana tafka fada tsakanin kabilu.

Ya zuwa yanzu kungiyar ta Taliban ba ta ce upon ba kan  mutuwar Mullah Salam Ahkund.

A watan Janairu shekarar 2017 ne Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar neman agaji Dala miliyan 550 domin taimakawa Afghanistan, wanda kashi 1 cikin 3 na al’ummar kasar ke cikin halin na tagayara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.