Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya kori jakadun wasu kasashe a Gambia

Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya kori jakadun wasu kasashe 12 daga kasar, bayan da suka bukaci ya mika ragamar shugabancin kasar ga Adama Barrow wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 1 ga watan jiya. 

Shugaba Yahya Jammeh na Gambia
Shugaba Yahya Jammeh na Gambia Photo: GRTS via AFP
Talla

Duk da cewa ba ta ambaci sunayen wadanda matakin ya shafa ba, to amma wata majiya a ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Gambia ta bayyana jakadun kasashen China da Birtaniya da Turkiyya da Senegal da kuma Amurka a matsayin wadanda aka bukaci su gaggauta barin kasar saboda sun aike da wasikun da ke yin kira ga shugaba Yahya Jammeh ya sauka daga karagar mulki.

Har ila yau jakadan kasar ta Gambia a Majalisar Dinkin Duniya na daga cikin jakadu 12 da suka rubuta wasikun taya murna ga Adama Barrow a kwanakin da suka gabata, kuma ana kyautata zaton cewa shi ma wannan mataki ya shafe shi.

To sai dai a sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Gambia ta ce, an bukaci jakadun da su gaggauta barin kasar ne saboda wa’adin aikinsu ya kawo karshe.

Kwana daya kafin wannan mataki dai, Amurka ta gargadi ‘yan kasarta da su guji zuwa Gambia domin ziyara ko kuma gudanar da wasu lamurra na yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.