Isa ga babban shafi
Gambia

Babban hafsan sojin Gambia ya jaddada biyayyarsa ga Jammeh

Babban hafsan sojin Gambia Janar Ousman Badjie ya ce zai ci gaba da yin biyayya ga shugaba Yahya Jammeh duk da barazanar da shugaban ke fuskanta daga kasashen duniya a yayin da wa’adin mulkinsa ke kawo karshe bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa.

Shugaba Yahya Jammeh na Gambia
Shugaba Yahya Jammeh na Gambia REUTERS/Carlos Garcia Rawlins/Files
Talla

A sakon sabuwar shekara da ya fitar sannan aka wallafa a wata jarida da ke kare manufofin gwamnatin kasar da ake kira Daily Observer, Janar Ousman ya ce za su ci gaba da yin biyayya ga shugaba Yahya Jammeh.

Kungiyar ECOWAS ta yi gargadin daukar matakan duk da suka dace domin tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 1 ga Disemba inda Adama Barrow na jam’iyyar adawa ya kada shugaba Jammeh.

Akwai dai alamun kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS na iya amfani da karfin Soji akan Jammeh idan har ya ki mika mulki ga Barrow.

Jammeh da ya shafe shekaru 22 yana mulki, ya yi amai ya lashe ne inda ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa tare da kalubalantar hukumar zaben Gambia mai zaman kanta a Kotu.

Masharhanta dai na ganin yadda hafsan hafsoshin sojin kasar ya fito ya tabbatar da biyayyarsa ga Jammeh babbar barazana ce ga makomar Gambia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.