Isa ga babban shafi
Gambia

Ba zan sauka daga kujerata ba- Jammeh

Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya yi watsi da yunkurin shugabannin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma na sasanta rikicin siyasar kasar,in da yake cewa babu abin da zai sashi ya sauka daga kujerarsa.

Shugaba Yahya Jammeh na Gambia
Shugaba Yahya Jammeh na Gambia REUTERS/Carlos Garcia Rawlins/Files
Talla

Shugaba Jammeh da ke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan sauya matsayinsa na kin amince wa da sakamakon zaben kasar, ya ce ba zai sauka daga kujerarsa a ranar 19 ga watan Janairu mai zuwa ba.

Jammeh ya ce, shi fa ba matsoraci bane kuma babu wanda zai tauye hakkinsa, ko razana shi ko kuma hana shi nasarar da ya samu sai dai Allah Mai Girma.

Shugaban wanda ke magana ta kafar talabijin din kasar, ya yi watsi da matsayin shugabanin kungiyar kasashen Afrika wanda ya ce, kafin su ziyarci Gambia don jin abin da ya faru, sun riga sun dauki matsayi cewar dole ya sauka daga mulki.

A bangare daya, kungiyar ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da tauna tsakuwa cewar, dole sai Jammeh ya sauka don bada damar rantsar da Adama Barrow a ranar 19 ga watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.