Isa ga babban shafi
Gambia

Shugaban hukumar zaben Gambia ya tsere

Shugaban hukumar zabe ta Gambia ya tsere daga kasar sakamakon barazanar rasa ransa kamar yadda dan dan uwansa ya sanar a yau Talata. 

Shugaban hukumar zaben Gambia, Alieu Momar Njai
Shugaban hukumar zaben Gambia, Alieu Momar Njai 路透社照片
Talla

A farkon watan Disamban da ya gabata ne, shugaban hukumar Alieu Momar Njai ya ayyana Adama Barrow a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugabancin kasar bayan da ya doke shugaba mai ci Yahya Jammeh.

To sai dai shugaba Jammeh ya ki amince wa da shan kayi bayan ya zargi jami’an hukumar zaben da tafka kura-kurai, abin da ya tilasta masa garzayawa kotu don kalubalantar sakamakon.

Tuni dai Mr. Njai mai shekaru 82 ya fice daga kasar bayan sha matsin lamba daga bangaren danginsa sakamakon barazanar hallaka shi har lahira.

A 'yan makwannin da suka gabata ne, jami’an tsaron Gambia suka mamaye hukumar zaben kasar tare da haramta wa ma’aika shiga cikin hukumar don gudanar da aikinsu, amma daga bisani sun janye.

Wannan dai na zuwa ne bayan Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta bukaci Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow a ranar 19 ga wannan wata na Janairu kamar yadda kundin tsarin mulikin kasar ya tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.