Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya yi amai ya lashe

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nuna cewa zai ci gaba da aiwatar da tsarin Shirin inshoran Lafiya na gwamnatin Barack Obama, bayan Sukar tsari da cewa zai Soke shi a lokacin yakin neman zaben shi.

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump
Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump REUTERS/Carlo Allegri
Talla

A zantawarsa da mujallar Wall Street Journal, ranar ta biyu a c igaba da aiwatar da sauye-sauye karban mulki, Trump ya ce zai iya ci gaba da aiwatar da wasu muhimman abubuwa da ke kunshe a shirin inshorar lafiyar.

A baya dai Trump ya bayyana shirin tamkar masifa ga kasar Amurka.

Tun bayan nasara Mista Trump da ta zo wa duniya da bazata, zabebben shugaban kasar yake ta sanar da sauye-sauye kan alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.