Isa ga babban shafi
Amurka

Ganawar Trump da shugabannin Republican

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya gana da shugabannin Jam’iyyarsa ta Republican a Capitol Hill domin dinke barakar da ke tsakaninsu bayan yawancin shugabannin Jam’iyyar sun juya ma shi baya a lokacin yakin neman zaben shi.

Donald Trump tare da Shugaban Majalisar Dattijai Mitch McConnell  à Washington.
Donald Trump tare da Shugaban Majalisar Dattijai Mitch McConnell à Washington. REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Duba da yadda Jam’iyyar Republican ta lashe zaben shugaban kasa tare da samun rinjayen kujeru a majalisar wakilai da dattijai, ake ganin ba wani babban kalubale ba ne ga Trump na hada kan ‘Yan jam’iyyar musamman wasu shugabanninta da suka ki mara mashi baya a yakin neman zaben shi.

Bayan ya gana da shugaba Obama a fadar White House, daga nan ne kuma Trump ya mika zuwa Capitol Hill inda ya tattauna da shugabannin Republican a jiya alhamis.

Trump ya shafe lokaci yana tattaunawa da kakakin majalisar wakilan Amurka Paul Ryan, bayan a watannin baya sun samu sabani inda har Ryan ya ki ya yi wa trump yakin neman zabe.

Amma kuma a ganawar Ryan ya nuna kamar babu abinda ya taba faruwa tsakanin shi da Trump.

Sannan Trump ya nemi goyon bayan ‘Yan Republican a majlisar domin cim ma alkawullan da ya dauka.

Sannan Trump ya gana da shugaban majalisar Dattijai MCConnell wanda ya fara nuna sukar manufar Trump na cim ma burin musanya shirin Obama na lafiya a kwanaki 100 na mulkinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.