Isa ga babban shafi
Amurka

An ci gaba da zanga-zangar adawa da Trump

Zanga-zangar adawa da nasarar Donald Trump a zaben shugabancin kasar Amurka ta shiga rana ta biyu, in da dururuwan mutane ke ci gaba da gangami a birane da dama da ke fadin kasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da Donald Trump a Amurka
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da Donald Trump a Amurka REUTERS/Eduardo Munoz
Talla

Akasarin masu zanga-zangar dai matasa ne, in da suka bayyana shugabancin Trump a matsayin abin da zai kawo rarrabuwar kawunan Amurkawa, baya ga nuna kabilanci da kuma banancin jinsi.

Rahotanni sun ce, zanga-zangar na neman rikidewa zuwa tarzoma a garin Portland da ke jihar Oregon, in da masu zanga-zangar suka yi ta fashe-fashe da kuma lalata kadarori, yayin da jami’an ‘yan sanda ke ci gaba da kokarin dakile su.

Baya ga Portland, babu rahotannin da ke nuna cewa an samu tarzoma a sauraren wuraren zanga-zangar da suka hada da New York Philadelphia da Chicago da Denver da Dallas da Oakland da kuma Baltimore.

To sai dai a martanin da ya mayar ta shafinsa na intanet, zababben shugaban, Donald Trump ya bayyana zanga-zangar a matsayin rashin adalci, sannan ya zargi kafafen yada labarai da tinzira jama’a.

A jiya ne dai, Trump wanda ya doke Hilary Clinton da gagarumin rinjaye a ranar Talata, ya gana da shugaba Barack Obama mai barin gado a fadar White House, in da suka zanta kan yadda za a mika mulki.

Mr. Trump dai ya bayyana Obama a matsayin mutumin kirki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.