Isa ga babban shafi
Amurka

Zaben Trump zai haifar mana da tsamin dagantaka-Juncker

Shugaban Tarayyar Turai EU, Jean Claude Juncker, yayi gargadin cewa zabar Trump a matsayin shugaban kasa na iya haifar da tsamin dagantaka tsakanin EU da Amurka.

Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump
Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Yayin da yake jawabi ga wasu dalibai a Luxemburg, Mr Juncker ya ce, tilas a yanzu jagororin EU su ilimantar da Trump sanin matsayin Turai da kuma tsarinta, muddin ana san ganin dai dai.

A cewar shugaban na EU, yana kyautata zaton za’ayi hasarar shekaru biyu ba tare da an cimma komai ba tsakanin EU da Amurka, saboda lokacin da Donald Trump zai bata yana ziyara kasashen Duniya domin fahimtar makamar mulki da alakar Amurka da kasashen.

Yayin yakin neman Zabensa a baya, Donald Trump, ya haifar da fargaba ga tarayyar Turai, musamman game da sukar rundunar tsaro ta NATO, da kuma barazanar janye sojin Amurka daga cikinta, sai kuma bukatar farfado da kyakkyawar alaka tsakanin Amurka da Rasha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.