Dole ne a dama da Turai a duniya- Mogherini
Shugabar diflomasiyar kungiyar kasashen Turai Federica Mogherini ta ce, kungiyar ta zama wata babbar nahiyar da ya zama dole a dama da ita wajen zaman lafiya a duniya.
Wallafawa ranar:
Yayin da take jawabi kan nasarar Donald Trump ta zama zababben shugaban Amurka, Mogherini ta ce, watanni ko kuma shekaru masu zuwa nan gaba, nauyin da ke kan Turai wajen wanzar da zaman lafiya tsakaninta da makwabtanta da kuma kawayenta zai dada karuwa.
Nasarar Donald Trump ta girgiza akasarin kasashen Turai saboda matsayinsa na sanya Amurka a gaba fiye da kowa da kuma shirin janye Amurka daga kungiyar tsaro ta NATO.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu