Isa ga babban shafi
Syria

MDD za ta sake tura kayan agaji zuwa Syria

Majalisar Dinkin Duniya za ta sake tura kayan agaji zuwa Syria duk da harin da aka kaddamar kan ayarin motocinta, yayin da cacar-baka ta kaure tsakanin Amurka da Rasha kan rikicin na Syria a zauren Majalisar.

Majalisar Dinkin Duniya za ta sake shigar da kayan agaji zuwa Syria
Majalisar Dinkin Duniya za ta sake shigar da kayan agaji zuwa Syria Fadi Dirani / AFP
Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ofishin kula da aikin jin-kai na Majalisar Dikin Duniya ya bayyana cewa, an dawo da shirye-shiryen shigar da kayan agaji zuwa yankunan da aka yi wa kawanya da kuma ke da wahalar shiga a Syria.

A ranar Litinin ne, ayarin Majalisar dauke da kayan agajin ya gamu da farmakin jiragen sama a dai-dai lokacin da yake sauke kayan agajin a wani gidan ajiye kaya na Orum-al-Kubra da ke birnin Aleppo.

To sai dai wannan farmakin ya haddasa cacar- baka tsakanin Amurka da Rasha bayan Washington ta zargi Moscow da da kaddamarwa.

Amma  Rashan ta musanta zargin cewa, jiragenta ko kuma na Syria ne suka kai harin.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bukaci a haramta wa jiragen yaki yin shawagi a muhimman wurare a Syria don sassauta fargabar kai farmaki, abin da kuma zai bada damar shigar da kayan agaji cikin sauki ga mabukata.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dai, na kokarin farfado da yarjejniyar da kasashen biyu suka cimma tare da shata hanyar kawo karshen yakin na Syria da ya kashe mutane fiye da dubu 300 cikin shekaru biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.