Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Amurka da Rasha na muhawara kan Syria

Amurka da Rasha sun shiga zazzafar muhawara kan rikicin Syria, a dai-dai lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke tattaunawar gaggawa kan lugudan wuta da ake yi a kasar, bayan mummunan harin da aka kai a birnin Aleppo kan kayan agaji.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ke gudanar da tattaunawar, bayan Washington ta zargi Moscow da kaddamar da harin  kan tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke dauke da kayan jin kai.

Sakatare janar na Majalisar, Ban ki-Moon  ya ce,  suna bincike don gano ainihin mai hannu a wannan harin kan fararan hula.

Ban ya ce, ya zama dole a sake dawo da yarjejeniyar tsaigata wuta a matsayin matakin farko da zai shawo kan yakin daya dai-daita Syria har tsawon shekaru biyar.

Sai dai Kerry, ya ce, tsaigata wuta ba za ta yiwu ba, har sai Rasha ta daina marawa dakarun Assad baya da kuma daukan alhakin harin Aleppo na ranar litinnin.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da ke sa’ido kan rikicin kasar ta bayyana yadda aka raba dare ana ruwan wuta a Aleppo da sauran yankunanan Syria tare da kashe jami’an kiwon lafiya da fararan hula da dama.

Bukatar Majalisar Dinkin Duniya ita ce, cimma daidaito da zai kawo karshan yaki tsakanin shugaba Assad da magoya bayansa da ‘yan tawayen kasar don samun damar shigar da kayan agaji, da hada kai don fatattakar kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.