Isa ga babban shafi
Syria

Yarjejeniyar Syria na cikin barazana

Yarjejeniyar tsagaita musayar wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Rasha na cikin wani hali, yayin da hare-haren jiragen sama da harbe-harben bindiga suka haifar mata da nakasu.

An kaddamar da hari a yankin Idlib a dai-dai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar Syria ke aiki
An kaddamar da hari a yankin Idlib a dai-dai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar Syria ke aiki AMEER ALHALBI / AFP
Talla

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da fararen hula ke ci gaba da zaman jiran kayayyakin agaji, yayin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, zai yi zama na musamman don nazari kan yiwuwar rattaba hannu kan yarjejeniyar.

An dai yi zaton yarjejeniyar za ta taka rawa wajen kawo karshen yakin da ya lakume rayukan mutane fiye da dubu 300, sai dai ta gamu da nakasu saboda yadda jinkirin shigar da kayan agajin da kuma ci gaba da samun tashin hankali a wasu yankuna har ma da rashin fahimtar juna tsakanin Washington da Moscow.

Kasar Rasha da ke mara wa shugaba Bashar al Assada na Syria ta bayyana cewa, a shirye take ta tsawaita yarjejeniyar wadda wa’adinta zai kare a yau jumma’a da sa’oi 72.

Sai dai Rashan ta caccaki Amurka da ‘yan tawaye da rashin mutunta yarjejeniyar.

Kananan yara guda biyu na cikin mutane uku da suka rasa rayukansu a yau jumma’a sakamakon hare-haren sama da aka kaddamar a garin Khan Sheikhun na Idlib wanda ke hannun ‘yan tawaye, kamar yadda kungiyar da ke sa ido a Syrian ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.