Isa ga babban shafi
Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta damu da rashin fara kai agaji a Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu babu wata tawagar jami’an kai kayan agaji da ta samu shiga kasar Syria, duk da shafe sa’o’i 48 da fara aikin yarjejeniyar tsagaita wuta.

Mutane a Syria sun fara samun nutsuwa
Mutane a Syria sun fara samun nutsuwa DELIL SOULEIMAN / AFP
Talla

Rahotanni sun ce har yanzu mahukunta basu kai ga cimma matsaya ba, game da hanyoyin da jami’an agajin zasu bi, wajen shiga yankunan da ke bukatar taimako.

A bangare guda kuma ma’aikatar harkokin waje ta Syria ta ce bazata bada damar kai gaji cikin birnin Aleppo ba, har sai ta san ido kan hakan, tare da jami'an Majalisar Dinkin Duniya.

Ma’aikatar wajen ta kuma jaddada cewa, bazata kyale motocin agaji na kasar Turkiya ketarawa cikin kasar ba.

Wata majiya mai tushe daga Syrian ta ce batun alakar gwamnatin Turkiya da rikicin kasar yana daya daga cikin dalilan da suka haifar da tsaikon fara shigar da kayan agaji zuwa sassan Syrian.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.