Rasha-Amurka
Halin da yarjejeniyar tsagaita wutar Syria ke ciki
Kasar Rasha ta zargi Amurka da kin nuna wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya takardun da ke dauke da bayanai kan yarjejeniyar tsagaita musayar wuta a Syria.
Wallafawa ranar:
Talla
A jiya ne dai, kwamitin tsaron ya soke zaman nazari kan yarjejeniyar saboda sabanin da ake samu tsakanin Amurka da Rasha.
Rahotanni sun ce, kwamitin ba zai goyi bayan yarjejeniyar ba da kasashen biyu suka cimma, har sai ya samu cikakkun bayanai kan abubuwan da ta kunsa.
An dai yi zaton yarjejeniyar za ta taka rawa wajen kawo karshen yakin shekaru biyar a Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu