Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya yi nadamar kalaman shi

Dan Takaran shugabancin Amurka a Jam’iyyar Republican Donald Trump ya bayyana takaicinsa da yadda ya ke batawa wasu mutane rai da irin kalaman da ya ke furtawa a lokacin yakin neman zaben shi.

Dan takarar Jam'iyyar Republican a zaben Amurka Donald Trump
Dan takarar Jam'iyyar Republican a zaben Amurka Donald Trump REUTERS
Talla

Trump da ke jawabinsa na farko bayan sake fasalin kwamitin yakin neman zabensa, ya ce wani lokaci idan kan shi ne ya yi zafi wajen mahawara ko kuma jawabi ya kan yi kuskure ga zabin irin kalaman da ya dace ya furta.

Dan takaran ya shaidawa gangamin yakin neman zaben shi a Charlotte North Carolina cewa lallai ya san yana furta munanan kalamai a baya, amma yanzu ya yi nadama sosai.

Musayar kalamun da Trump ya yi da iyayen wani Sojan Amurka da aka kashe a Iraqi, shi ne ya fi jan hankali a yakin neman shi.

Sannan da yadda ya ke caccakar abokiyar hamayyar shi Hillaty Clinton, inda masu sharhin siyasar Amurka ke ganin Trump na kokarin hura wutar rikici ne a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.