Isa ga babban shafi
US

Dan Bindiga Ya Nemi Shiga Fadar Shugaban Amurka

Jami'an tsaron fadar Shugaban kasar Amurka White House na chan suna binciken musabbabin da ya kai wani mutun kusa da fadar Shugaban kasar har ya yi harbi da bindiga jiya Juma'a. 

Shugaban Amurka Barack Obama  gaban hoton fadar shugaban
Shugaban Amurka Barack Obama gaban hoton fadar shugaban REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Bayanai na nuna Shugaban Amurkan Barack Obama baya kusa da fadar a lokacin da aka kwashe awa daya ana cikin wani hali a harabar fadar Shugaban kasar, amma daga bisani an shaida masa abinda ya faru.

Robert Hoback, kakakin fadar ya bayyana cewa mutumin tunkarar fadar yayi da bindiga yana harbi, amma kuma jami'an tsaron fadar sunyi ta maza, bayan da suka yi ta daka masa tsawa mutumin ya ki ji, nan take wani Jami'in tsaro ya bindige mutumin amma bai mutu ba nan take, an kwashe shi zuwa asibiti.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.