Yan Majalisan Dattawan Brazil sun tsige shugabar kasar Dilma Roussef
Yan Majalisar Dattawan Brazil 55 sun bayyana goyan bayan su na dakatar da shugabar kasar Dilma Rousseff bayan kwashe sa’oi 17 ana tafka mahawara.Majalisar bayan kada kuri'a ta amince da batun tsige shugabar kasar Dilma Roussef mai shekaru 68.Bangaren Uwargida Dilma Roussef sun bayyana cewa juyin mulki ne aka yiwa Dilma Roussef .
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majalisar dattawan kasar bayan tafka mahawara kan shirin dakatar da shugabar kasar Dilma Rousseff saboda zargin da ake mata na almundahana da kuma cin hanci da rashawa ta amince da batun tsige ta,mataimakin Shugabar Michel Temer ne zai maye gurbin Uwargida Dilma na tsawon watanni shida. .
Michel Temer mai shekaru 75 ne zai jagoranci Brazil,tareda yi kokarin gani ya hada kawunan yan siyasa dama yaki da cin hanci da rashawa.
Bayan kamala shari’ar da za’ayi mata Majalisar zata nemi kuri’u biyu bisa uku dan tsige ta baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu