Isa ga babban shafi
Amurka-IS

Amurka za ta kara kudi a yaki da ISIS

Kawancen kasashen da Amurka ke jagoranta domin yaki da kungiyar ISIS ya sake bayyana aniyarsa ta kara sanya kudade a yakin domin ganin an yi nasarar murkushe mayakan kungiyar.

Sakataren harkokin tsaron Amurka, Ashton Carter
Sakataren harkokin tsaron Amurka, Ashton Carter 法新社
Talla

Alkawarin ya biyo bayan taron da aka gudanar a Stuttgart da ke kasar Jamus wanda ya kunshi ministocin tsaron kasashen kawancen a karkahsin Ashton Carter na Amurka.

Taron ya bayyana shirin girke kayan yaki nan bada dadewa ba don ganin bayan kungiyar.

Kasashen da suka halarci taron sun hada da Australia da Birtaniya da Canada, sauran sun kunshi Denmark da Faransa da Jamus da Italiya da New Zealand da Norway da Spain.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.