Carter na Amurka na ziyara a Iraqi
Sakataren tsaron Amurka Aston Carter ya kai ziyara birnin Bagadaza domin tattaunawa da hukumomin Iraqi akan mayakan kungiyar ISIS mai da’awar jihadi.
Wallafawa ranar:
Ziyarar Carter na zuwa ne bayan mako guda da Iraqi ta tsindima cikin rikicin siyasa, abinda ya zama koma baya ga Firaministanta Haider al-Abadi yayin da Amurka ta ce, akwai bukatar tallafa wa Firaministan.
Mr. Carter zai gana da ministan tsaron Iraqi, Khaled al-Obeidi, inda za su zanta kan yiwuwar karin tallafin soji da Amurka za ta bai wa Iraqi gabanin fafatawar da za a yi a birnin Mosul.
Amkurka ce dai ke jagorantar dakarun kawance da ke kaddamar da hare haren sama kan kungiyar ISIS tare da horar da dakarun da ke fada da mayakan a Iraqi da Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu