Isa ga babban shafi
Amurka

ISIS ta kashe dubban 'yan Shi'a da Kiristoci a Iraqi

Kasar Amurka ta bayyana cewa kungiyar ISIS ta aikata kisan kiyashi kan dubban Musulmai 'yan Shi’a da mabiya mazhabar Yazidi da kuma Kiristoci a kasar Iraqi, amma sai dai Amurkan ta ce za ta kawo karshen wannan aika aika.

Amurka ta ce, kungiyar ISIS ta kashe dubban mabiya Shi'a da Yazidi da kuma Kiristoci a Iraqi
Amurka ta ce, kungiyar ISIS ta kashe dubban mabiya Shi'a da Yazidi da kuma Kiristoci a Iraqi © REUTERS/Stringer
Talla

Wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerrry ya fitar ta nuna yadda kungiyar ta Daesh ko kuma ISIS ta yi wa mabiya Shi’ar kisan kiyashi da nufin cimma nata bukatun irin na ta’addanci.

To sai dai sanarwar ba ta bayyana irin matakin da Amurkan za ta dauka ba, amma dai akwai tabbacin cewa Washinton na aiki tukuru don samun cikakkun hujjojin shiga gaban kuliya.

A shekara ta 2014 dai kungiyar ta ISIS ta kama garin Masoul da ke arewacin Iraqi, inda aka rika yi wa mutanen garin kisan gilla tare da fyade ga mata, baya ga bautar da matasa.

Kungiyar dai inji sanarwar ta yi amfani da matasan da ta kama ne wajen mayar da su mambobinta, tare kuma da amfani da su wajen kisan kiyashi kan 'yan kabilar Yazidi da kuma ‘yan Shi’a, abinda inji sakataren harkokin wajen Amurkan John Kerry za su ci gaba da yaka, ta hanyar hare haren da suke kai wa kungiyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.