Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta bukaci a kara kaimi wajen yaki da ISIS

Kasar Amurka ta bukaci kawayenta da su kara kaimi a yakin da su ke yi da kungiyar ISIS a Iraqi da Syria yayin da ta bayyana shirinta na tallafa wa dakarun Iraqi da jiragen yaki masu saukar ungulu.

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter
Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter REUTERS/Yuriko Nakao/Files
Talla

Sakataren tsaron Amurka ne Ashton Carter ya sanar da haka kuma ya bayyana jerin shirye shiryen sojin kasar na kara kaimi wajan yaki da ISIS din bayan hare haren da aka kai a birnin Paris na Faransa da San Bernardino na jihar California da ke Amurka.

Carter ya ce, dole ne kasashen duniya su zage danze tun da wuri kafin a kaddamar da wani mummunan harin irin wanda aka gani a Paris, inda mutane 130 suka rasa rayukkansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.