Isa ga babban shafi
Faransa

Harin Paris: Faransa ta sake gano wani matashi

Hukumomin Faransa sun bayyana wani matashi a matsayin mutun na uku da ke da hannu a hare haren ta’addancin da kungiyar ISIS ta kai a birnin Paris, inda mutane 130 suka rasa rayukansu.

Jami'an tsaron Faransa
Jami'an tsaron Faransa REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Ana kyautata zaton Foued Mohamed Aggad mai shekaru 23 na da hannu a harin da aka kai a gidan rawa na Bataclan kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar a yau laraba.

Rotanni sun ce, Aggad ya tafi kasar Syria tare da dan uwansa da wasu abokansa a karshen shekara ta 2013, kuma jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu daga cikin su bayan sun dawo Faransa a bara amma Aggad na can zaune a kasar Syria.

Mutane 90 ne dai suka rasa rayukansu a gidan rawan na Bataclan daga jumullan mutane 130 da hare haren na Paris suka kashe.

Tuni dai aka bayyana sauran maharan biyu da suka hada Omar Omar Isma’il Mostefani mai shekaru 29 da kuma Samy Amimour mai shekaru 28.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.