Isa ga babban shafi
Faransa

An bude mashayar Paris bayan harin ta'addanci

An sake bude mashayar La Bonne Biere, inda aka kashe mutane biyar a hare haren ta’addancin da aka kaddamar a birnin Paris na kasar Faransa.

Talla

Wannan dai wani mataki ne dangane da kokarin da al-ummar kasar ke yi na maido da ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba gabanin harin wanda kungiyar ISIS ta ce, ita ta kaddamar.

Wani mutum mai suna Valentine wanda ya saba wucewa ta gaban mashayar ya bayyana cewa, sake bude ta abune mai kyau, sai dai za a ci gaba da tunawa da mummunan abinda ya faru a wurin.

Ita kuwa Aliette wadda saurayinta ya rasa dansa a harin, cewa ta yi, mikin da harin ya yi wa jama’a ba zai taba warkewa ba.

Hare haren dai na ranar 13 ga watan Nuwamban da ya gabata sun yi sanadiyar mutuwar mutane 130, al-amarin da ya girgiza al-ummar Faransa da manyan kasashen duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.