Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta kai wa IS hare hare a Iraqi da Syria

Faransa ta kai wasu jerin hare-hare da wani Shahararren jirgin yakinta, Charles de Gaulle kan makwancin kungiyar IS masu ikirarin jihadi a kasar Iraqi da Syria.

Jirgin Charles-de-Gaulle na Faransa
Jirgin Charles-de-Gaulle na Faransa REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Babban Hafsan Sojan d ake kula da shu’umin jirgin yakin, Janar Pierre de Villiers ya fadi cewa jirgin yakin Faransa mai dakon sauran jiragen yaki ya kai hari yankunan Ramadi da Mosul domin taimakawa sojan kasa fatattakan mayaka masu jihadin.

Yace jiragen da ke cikin Charles De Gualle zasu kai hare-hare kan cibiyar diban sabon shiga masu jihadin, da kuma wuraren da suke adana mai, da dai wasu muhimman wurare da masu jihadin ke takama da su.

Hare-haren daga wannan jirgin dakon jiragen yaki na zuwa ne kwanaki 10 bayan mummunar harin da kungiyar IS ta masu jihadin suka kai Paris na Faransa, inda mutane samada 130 suka mutu.

Tuni, Shugaban Faransa Francois Hollande ya furta cewa zasu zafafa kai hare-haren zuwa kan masu ikirarin jihadin har sai sun share su baki daya.

Kananan jiragen yaki akalla 26 ke cikin wannan jirgin dakon jiragen yaki daga Faransa, duk wadannan baya ga tarin wasu jiragen yakin ne dake ta luguden wutan a Syrian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.