Isa ga babban shafi
Faransa

An tantance maharan Paris 5

Masu bincike a kasar Faransa sun gano mutane 5 daga cikin 7 da suka kai hare hare a birnin Paris, yayin da ake ci gaba da neman sauran. Binciken ya nuna cewar daukacin mutanen Faransawa ne da suka hada da Omar Ismaila Mostefai da Samy Amimour da Brahim Abdeslam da Salah Abdeslam da Bilal Hafdi da Ahmad al Mohammed.

Mutane 129 aka kashe a munanan hare haren da aka kai a Paris a ranar Juma'a
Mutane 129 aka kashe a munanan hare haren da aka kai a Paris a ranar Juma'a Anne Bernas/RFI
Talla

Omar Ismail Mostefai da Samy Amimour su suka kai harin kunar bakin wake a wani gidan cashewa na Bataclan inda aka bindige mutane 89 a ranar Juma’a.

An haifi Mostefai ne a Paris a shekarar 1985, kuma masu bincike sun ce ya taba zuwa kasar Syria a 2014. Da dadewa Turkiya ta aika da sakon gargadi ga Faransa akan Mostefai amma kasar na watsi da gargadin na Turkiya.

Brahim Abdeslam da Salah Abdeslam, ‘yan uwan juna ne da suka kai hari a wata mashaya ta Boulevard Voltaire a Paris.

Bilal Hadfi da Ahmad al-Mohammad su suka kai hare haren kunar bakin wake a kusa da filin wasan kwallon kafa a lokacin da Faransa da Jamus ke buga wasan sada zumunci.

Ahmad al Muhammad ne jami’an tsaro suka tsinci fasfo din kasar Syria a kusa da gawar shi, wanda aka gano dan asalin garin Idlib ne a Syria.

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike domin tantance fasfo din bayan mahukuntan Serbia sun kame wani dan gudun hijira mai dauke da Fasfo irin na maharin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.