IS
An kashe mayakan IS 32 a Syria
Akalla mayakan IS 32 aka kashe a Syria a wasu hare haren jiragen yakin Amurka da kwayenta suka kai a yankin Raqa a yau Lahadi. Akalla wasu kimanin 40 suka jikkata a hare haren da aka kai a sansanin IS, kamar yadda Kungiyar da ke sa ido a rikicin Syria ta tabbatar.
Wallafawa ranar:
Talla
Tun munanan hare haren da aka kai a Paris, Amurka da Faransa suka zafafa hare hare akan IS.
Kuma yanzu Birtaniya da Jamus sun shiga kawancen na farwa mayakan na IS da ke da’awar jihadi a Syria da Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu