Amurka
IS ta jinjinawa maharan California
Kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a duniya tace makayakanta ne suka kai hari a California inda aka kashe mutane 14 tare da jikkata wasu 21 a ranar Laraba.
Wallafawa ranar:
Talla
A cikin wani sakon da kungiyar ta yada a kafar rediyonta na Inglishi, kungiyar ta dauki alhakin harin na San Bernardino tare da yin jinjina ga maharan biyu mata da miji da kungiyar ta kira Sojojin daularta.
Hukumar FBI tace maharan sun yi alaka da mayakan IS a intanet. IS kuma tace ita ta sa aka kai harin a California.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu