Obama zai tura Karin dakaru a Syria
Shugaba Barack Obama ya ce Amurka za ta tura Karin dakaru sama da 250 da wasu manyan jami’an Soji zuwa Syria domin taimakawa ‘Yan tawaye yakar mayakan IS da ke da’awar Jihadi.
Wallafawa ranar:
Mista Obama ya fadi haka ne a Hanover a Jamus a taron tattaunawa barazanar IS tsakanin shi da shugabannin kasashen Jamus da Birtaniya da Faransa da kuma Italiya.
Shugabannin za su tattauna yadda za su hada kai domin yakar mayakan IS da suka yi ikirarin kaddamar da sabuwar daula a wasu yankunan kasashen Syria da Iraqi da suka kwace.
Obama yace Amurka ba zata jagoranci yaki a kasa ba amma dakarunta za su bayar da horo na musamman ga dakarun Iraqi da ke fada da IS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu