Koriya ta Arewa Ta Sake Gwajin Wani Shu'umin Makami
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya bayyana cewa kasar sa ta yi nasarar gwajin wani shu'umin makami mai linzami, wanda zai iya yin barna a kasashe makwabciyar ta Koriya ta Kudu da kuma kasar Amurka.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne jim kadan da kasar Koriya ta Arewa ta yi tayin cewa idan har ana son ta daina gwajin makamai na nukiliya sai kasar Amurka ta daina atasayen soja da makamai da take yi tare da Koriya ta Kudu.
Amurka da Britaniya sunyi Allah wadai da gwajin na baya-bayan nan kamar yadda ta saba yi da gwaje-gwajen makamai na baya.
Rahotanni na cewa shugaban kasar Korea ta Arewa da kansa ya ke sa idanu yayin gwajin makaman da akayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu