EU ta yaba da matakin gwamnatin Syria kan Madaya
Kungiyar tarayyar Turai ta yi marhaba da matakin gwamnatin Syria na amincewa da isar da kayayyakin jin-kai ga al-ummar garin Madaya da ke fama matsanacin yunwa yayin da ta bukaci a daina kai hare hare kan fararan hula a rikicin da ake yi a kasar.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacon da ake shirin gudanar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Syria da ‘yan tawaye a ranar 25 ga wannan watan da nufin kawo karshen rikicin kasar.
A cewar Federica Mogherini, shugabar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, matakin da Assad ya dauka na a matsayin wani ci gaba dangane da samar wa al-ummar Madaya mafita daga matsancin halin da suka samu kansu a ciki saboda yakin Syria.
Yakin Syria dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 250 a cikin shekaru biyar da suka gabata, lamarin da ya haifar da koma baya matuka ga kasar wadda a yanzu ta zama sansanin horar da masu tayar da kayar baya.
Bayanai dai sun tabbatar da cewa, mutane da dama ne ke mutuwa a dalilin yunwa a yankunan madaya da Foua da Kefraya, sai dai abin ya fi kamari a madaya wanda aka yi wa kawanya.
Kimanin mutane dubu 40 ne galibin su fararen hula ke zaune a madaya cikin yunwa da kishin ruwa, har ta kai suna cin kwari da ganyaryaki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu