An kashe jagoran ISIS da ke da hannu a harin Paris
Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa wani shugaban kungiyar ISIS da ke da hannu a hare haren da aka kaddamar a birnin Paris na kasar Faransa, na cikin jiga-jigan kungiyar 10 da aka kashe cikin wannan watan a Syria da Iraqi.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun rundunar Amurka da ke yaki a Iraqi, Kanar Steve Warren ya shaida wa manema labarai cewa an kashe Charraffe el-Mouadan a hare haren jiragen sama da rundunar hadin gwiwa karkashin jagorancin Amurka ta kai a ranar 24 ga wannan wata na Disamba.
Amurka dai na zargin Mouadan da shirya kaddamar da wasu hare haren nan gaba a kasashen Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu