Isa ga babban shafi
Faransa

Za a gyara kundin tsarin mulkin Faransa don fada da ta’addanci

Gwamantin Faransa, ta amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara domin fada da ayyukan ta’addaci. Wani sashe na daftarin dokar ya bayar da damar kwace wa dan asalin kasar Faransa shaidar zama dan kasa matukar dai aka same shi da laifin aikata ta’addanci.

Firaministan Faransa Manuel Valls
Firaministan Faransa Manuel Valls REUTERS/Eric Feferberg/Pool
Talla

Firaministan kasar Manuel Valls, ya ce samar da dokar ya zama wajibi.

A cewarsa barazanar ta’addanci ta kara tsananta, don haka dole ne a samar da dokokin da za su tanadi daukar matakan da suka dace.

“dole ne mu samar da dokoki wadanda za mu yi amfani da su a tsawon shekaru masu zuwa” inji Valls

Sai dai kuma yace samar da irin wadannan dokoki ba ya nufin za a kaucewa hanyoyin da suka tanadi kare hakki da mutuncin dan adam.

Ya kara da cewa mutunta doka shi ne babban makamin da ake iya yin amfani da shi wajen gina dimokuradiyya.

Faransa dai na fuskantar barazana daga Mayakan IS wadanda suka dauki alhakin jerin hare haren da aka kai a Paris a ranar 13 ga watan Nuwamba inda aka kasha mutane 130.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.