Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta biya diyya na €300m ga wadanda suka yi rashi a harin Paris

Gwamnatin Faransa ta sanar da ware kudi Yuro miliyan 300 a matsayin diyya ga iyalan  wadanda suka rasa ‘yan’uwa ko wadanda  harin Ta'addancin da aka kai a birnin Paris ya shafa.

Bataclan,daya daga cikin wurarren da aka kai hari a Paris
Bataclan,daya daga cikin wurarren da aka kai hari a Paris
Talla

Ministar  shari’ar kasar Faransa Christiane Taubira tace akalla gwamnatin kasar zata kashe kudin da suka kai yuro miliyan 300 wajen biyan diyya ga iyalai da kuma wadanda harin birnin Paris ya ritsa dasu

Taubira ta bayyana kokarin da gwamnatin Faransa ke yi na ganin an takaita wahalhalun da ‘yan’uwan mamatan suka shiga bayan harin tare da biyan diyya ga sauran iyalan mamatan.

Ta kuma ce gwamnati za ta cika alkawuran da ta dauka kamar dai yadda dokar kasar ta bukaci a yi a irin wannan yanayi.

Ministar dake hira da wata jaridar kasar mai suna Le Parisien ta bayyana yadda hukumomin kasar suka fuskanci matsalloli kama daga magada ko mutanen da al’amarin ya shafa bayan harin da ya kasance mafi muni da aka taba kaiwa a kasar.

An kayyade akalla Yuro 40.000 zuwa Yuro 600.000. da za’a baiwa ‘yan kasuwa da kananan masana’antu.

Gwamnatin Faransa na sa ran kashe kudin da suka kai Yuro milliyan 300 a biyan dirya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.