Isa ga babban shafi
Syria

Yunwa na kashe mutane a yankuna Syria

Gwamnatin Syria ta bada damar kai taimakon jin kai wasu yankunan kasar uku da aka bada rahoton mutane na mutuwa sakamakon yunwa.Tuni dai Majalisar dinkin duniya tayi marhaba da wannan mataki da ta ce zai ceto rayukan jama’a.

REUTERS/Feisal Omar
Talla

Bayanai dai sun tabbatar da cewa mutane da dama ne ke mutuwa a dalilin yunwa a yankunan madaya da fua da kafraya, sai dai abun yafi kamari ne a madaya inda mutanen da ba a hakikan ce adaddin su ba ke mutuwa wasu kuma ke cikin mawuyacin hali.

Daga ciki dai akwai wani mutum dan shekaru 53 daya mutu a ranar talatar data gabata, sakamakon bakar yunwar da ta kassara shi.

Garuruwan Uku dai na cikin yankunan da abaya akayi yarjejeniyar tsagaita wuta don bada damar shigar da kayan jin kai.

Garin Madaya dai na makwabtaka ne da zabadani, da dakaraun Gwamnati suka killace, yayinda fua da kafraya dake a arewacin kasar ke hannun mayakan dake adawa da gwamanatin shugaba Bashar al-Assad.

A lokacin da’aka samu labarin kai taimakon abincin mutane sunyi ta harb- harbe a cikin iska yayin da dadama kuma ke dakon ganin gaskiyar lamarin.

Kimanin mutane dubu 40 ne galibin su fararen hula ke zaune a madaya cikin mawuyacin halin yunwa da kishin ruwa, da hattakai suna cin kwari da ganyaryaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.