Isa ga babban shafi
Amurka-China

Obama ya bukaci China ta daina gina sabbin tsibirai

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya bukaci kasar China da ta daina gina sabbin tsibirai a gabar ruwan da ta ke rikicin da kasashen dake makwabtaka da ita.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama.
Talla

Yayin da yake jawabi wajen taron shugabanin kungiyar Asia-Pacific, shugaba Obama ya ce sun tattauna da shugaban Philippines Benigno Aquino kan illar da matakin na China ke haifar wa a Yankin da kuma barazanar tsaro.

Shugaban ya kuma sanar da taimakon Dala miliyan 250 da jirgin ruwan yaki dan taimakawa kawayen Amurka da ke Yankin.

China na rikici da kasashen Philippines, Vietnam, Malaysia, Brunei da Taiwan kan mallakar gabar ruwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.