Isa ga babban shafi
Amurka-Kenya-Habasha

Obama ya yi gargadi kan munanan dabi'u a Afrika

Yayin kammala ziyarar sa a kenya, idan yanzu haka ya isa kasar Habasha shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gargadi al'ummar kasashen gabashin Afrika da su sauya halayarsu domin kaucewa hatsari.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama Yayin bankwana da al'ummah a Nairobi, Kenya
Shugaban kasar Amurka Barack Obama Yayin bankwana da al'ummah a Nairobi, Kenya Reuters
Talla

Batun cin hanci da rashawa, nuna kalibalanci da kuma rashin dai-daito sune manya batutuwa da Barack Obama ya gargadi al'ummar Afrika domin kaucewa hatsari dake tatare da yin haka.

Kalaman Obama da ke zuwa a matsayin sakonsa na karshe kafin ficewar sa daga birnin Nairobi na Kemya, ya ce ya zama tilasn kuma a kauracewa al’adu da dabi’u marasa kyau, Musamman rikice-rikice tsakanin juna da yiwa ‘ya’ya mata Shayi da cin zarafinsu.

Tuni dai aka tsaurara matakan tsaro a birnin Habasha na Addis Ababa, Inda Barack Obama zai kammala ziyarar ta shi na kwanaki biyu da ya kawo gabashin Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.