Obama ya yaba da ci gaban da ake samu a nahiyar Afrika
Yau Asabar, shugaban Amurka Barack Obama dake ci gaba da ziyara mai cike da tarihi a kasar Kenya, na ganawa da mahukuntan kasar, kan batutuwan da suka shafi ciniki da zuba jari, gami da yaki da ta’addanci da kuma kare hakkin dan Adam.
Wallafawa ranar:
Shugaban, dake jawabi a wajen wanin taron bunkasar kasuwanci, ya yaba da yadda nahiyar Africa ke samun ci gaba cikin gaggawa, inda yace ana ana samun bunkasar zuba jari a nahiyar.
Mr. Obama yace mutanen Africa suna samu suna ficewa daga kangin talauci, kudaden shiga na karuwa, ta yadda masu matsakaicin karfi ke samun ci gaba, matasa kuma suna samun ci gaba a bangaren kimiyya don bunkasar harkokin kasuwanci.
Tattaunawar da Obama zai yi da mahukuntan kasar zata mayar da hankali kan barazanar kungiya al-Shebab ta Somalia, mai alaka da Al-Qaeda, da tayi ta kai hare hare a kenya, har da wanda aka hallaka dalidai a wata jami’ar kasar cikin watan Aprilu.
An karfafa matakan tsaro a ciki da wajen birnin Nairobi, inda ofishin jakadancin Amurka a birnin Nairobi ke cewa ‘yan ta’adda zasu iya neman kai farmaki a wajen taron.
Wannan ce ziyararsa ta farko a Kenya, da ita ce tushen mahaifinsa, inda kuma ake sa rai gobe Lahadi zai wuce zuwa kasar Ethiopia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu